12 Yuli 2021 - 12:23
​Iran Ta Yaba Da Kyakkyawar Alaka Da Ke Tsakaninta Da Al'ummar Bosnia

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya bayyana cewa kasar Iran ta na alfahari da kasancewa tare da mutanen Bosnia da Herzegovina tun lokacin samun ‘yancin kan kasar daga tsohuwar tarayyar Yugoslaviya.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya nakalto zarif yana fadar haka a sakon da ya aikewa taron tunawa da kisan kiyashin Srebrenica karo na 26 wanda aka gudanar a jiya Lahadi.

Ministan ya bayyana takasicinsa da kissan kiyashin na Bosniya a shekara 1995, ya kuma kara da cewa, kisan kiyashin ya na daga cikin munanan al-amura da suka faru a cikin tarihin nahiyar Turai da kuma duniya gaba daya, wanda ba za’a taba manta da shi ba.

342/